News
Ba Za A Gudanar Da Zaɓen Gwamna A Jihohi 8 Ba
Ba za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Imo, Ondo, Osun, Bayelsa, Edo, Kogi, Ekiti da Anambra tare da sauran jihohin da za su gudanar da zaɓen gwamna a babban zaɓen 2027 ba, saboda jadawalin zaɓensu ya bambanta da na sauran jihohin.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026, aka buɗe lokacin yaƙin neman zaɓen gwamna da na ’yan Majalisun Dokokin Jihohi, bisa jadawalin da ta fitar na zaɓen 2027.
An Buɗe Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna Da Majalisun Jihohi A Najeriya
Jihohi 28 ne za su gudanar da zaɓen gwamna a shekarar 2027, inda ’yan takara daga jam’iyyun siyasa za su fara gabatar da manufofinsu ga masu zaɓe tare da neman ƙuri’unsu.
Za a gudanar da yaƙin neman zaɓen ta hanyoyi daban-daban, ciki har da tarukan siyasa, kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyin da dokar zaɓe ta amince da su.
Daga cikin manyan jam’iyyun siyasar da suka tsayar da ’yan takarar gwamna a jihohin da za su gudanar da zaɓen akwai APC, NDC da ADC.
Sai dai, wasu daga cikin manyan jam’iyyun siyasar har yanzu ba su kammala kafa ko ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓensu ba, duk da fara lokacin kamfen.
Rahotanni sun ce jam’iyyar APC na sake nazarin wasu daga cikin naɗe-naɗen da ta yi a kwamitin yaƙin neman zaɓenta, biyo bayan koke-koke da aka samu kan wasu mambobin kwamitin.
Haka kuma, jam’iyyun NDC, ADC da PDP ba su kammala ƙaddamar da wasu daga cikin tsare-tsaren yaƙin neman zaɓensu ba.
Masana harkokin siyasa sun danganta jinkirin da wasu jam’iyyun ke fuskanta da rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓukan fidda gwani, ƙarancin kuɗaɗen gudanar da kamfen da kuma tattaunawar ƙulla ƙawance gabanin babban zaɓen.
A cewar jadawalin INEC, an fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ’yan Majalisar Tarayya tun ranar 19 ga Agusta, 2026.
