News
Na Siyar Da Tagwayen Jarirai Maza Kan Naira Dubu 300 — Wacce Ake Zargi
Wata mata mai shekaru 50 da ’yan sandan jihar Oyo suka kama bisa zargin hannu a satar yara da safarar su, ta ce ta sayar da jariranta tagwaye maza kan Naira 300,000.
Matar mai suna Adejoke Popoola, wadda aka fi sani da Orente Alagbo, ta kuma yi ikirarin cewa ta taba satar wasu yara tare da kai su hannun mutanen da ake zargin suna gudanar da sana’ar safarar jarirai.
APC na Fuskantar Babban Kalubale a Adamawa Yayin da Abdulrahman Haske ke Shirin Komawa APM
A cikin wani faifan bidiyo da Oyo Affairs ta wallafa, Popoola ta ce ta sace akalla yara 13, inda ta ke karɓar tsakanin Naira 80,000 zuwa Naira 120,000 kan kowane yaro da ta kai wa waɗanda take zargin suna harkar.
Ta ce ta shiga wannan harkar ne bayan ta haɗu da wata mata mai suna Oluwakemi, wadda ta ce tana gudanar da wata cibiyar safarar jarirai tare da kai su ga masu saye a Legas.
Popoola ta ce a bara ta sayar wa matar wani ɗanta mai shekara guda, sannan ta sake sayar mata da tagwayen da ta haifa, inda ta ce an ba ta Naira 300,000.
Ta kuma bayyana yadda ta sace wani yaro mai shekaru uku mai suna Ifakunle Ifagbenro a yayin wani bikin Egungun a Oyo a watan Yuni.
A cewarta, ta nemi mahaifiyar yaron ta ba ta damar ɗaukar shi, kafin daga bisani ta gudu da shi. Ta yi ikirarin cewa daga baya an biya ta Naira 900,000 kan yaron.
Matar ta kuma yi ikirarin cewa a wasu lokuta tana yaudarar iyalai masu yara masu nakasa, tana yi musu alkawarin za ta taimaka wajen warkar da ’ya’yansu, sannan ta ɗauki wani yaro ta ba su.
Popoola ta ce a baya tana sana’ar sayar da magungunan gargajiya, amma bayan gobara ta lalata shagonta a watan Janairun 2024, ta shiga cikin harkar satar yara.
Ta ce mutanen da ta haɗu da su a wannan lokacin ne suka shawarce ta da ta dinga satar yara domin ta riƙa kai musu, inda ta fara karɓar Naira 80,000 kan yaro kafin kuɗin ya koma tsakanin Naira 80,000 zuwa Naira 120,000.
A halin da ake ciki, ’yan sandan Oyo sun ce binciken da suka fara bayan samun ƙorafi ya bankado wata babbar hanyar satar yara, safarar su da sayar da su.
Rundunar ta ce kawo yanzu ta ceto yara 17 tare da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da aka samu rahoton mutuwar wasu yara shida a lokacin da suke hannun waɗanda ake zargi.
’Yan sandan sun kuma ce binciken ya nuna yiwuwar alaƙar wasu daga cikin waɗanda ake zargin da ayyukan tsafi, inda aka gano zargin sayar da gawarwakin wasu yaran da suka mutu ga masu aikata tsafi.
-
News6 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days agoDSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

