News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Cif Sufuretandan Bogi A Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Adamu Musa, mai shekaru 35, bisa zargin yin sojan gona da kuma damfarar jama’a da sunan babban jami’in ’yan sanda.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Kotu Ta Daure Mutane Biyu Shekara 9 Kan Bai Wa Yara Abubuwan Maye A Kano
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 1 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 7:30 na dare, bayan rundunar ta samu rahoto da bayanan sirri daga sashen ’yan sandan Panshekara.
A cewar sanarwar, Adamu Musa ya kasance yana gabatar da kansa a matsayin CSP, yana kuma yaudarar mutane da cewa yana da damar samo musu aikin ’yan sanda da kuma sauya musu wuraren aiki.
Rundunar ta ce wanda ake zargin ya yi amfani da hotunan da aka gyara da kuma fasahar AI, inda ya haɗa hotonsa da na wasu manyan jami’an ’yan sandan Najeriya domin ya sa mutane su yarda da ikirarinsa.
An kuma ce ya yi amfani da sunayen wasu manyan jami’an tsaro wajen karɓar kuɗi daga mutane, da sunan zai taimaka musu wajen samun aikin ’yan sanda ko sauya wuraren aikinsu.
Kakakin rundunar ya ce yayin binciken gidan wanda ake zargin, jami’an tsaro sun gano uniform guda ɗaya, takalman baƙi guda biyu, kayan camouflage guda ɗaya, rigar uniform mai shuɗi guda ɗaya da kuma N300,000.
Ya ce wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ta gargadi jama’a da su yi hattara da masu kwaikwayon jami’an tsaro da masu amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar hotunan bogi domin yaudarar mutane da karɓar kuɗi.
Ta kuma buƙaci jama’a da su kai rahoton duk wani mutum da ke gabatar da kansa a matsayin jami’in tsaro ba tare da sahihin bayani ba.
