News
An Kama Mage Tana Safarar Miyagun Kwayoyi Zuwa Gidan Yari
Hukumomin kula da gidajen yari na ƙasar Rasha sun kama wata mage da ake zargin an yi amfani da ita wajen safarar miyagun ƙwayoyi zuwa wani gidan gyaran hali da ke yankin Nizhny Novgorod.
Jami’an tsaron gidan yarin sun ce sun tare magen ne a ranar 21 ga watan Yuli, bayan sun gano tana ɗauke da wasu ƙananan kunshe-kunshen miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye cikin wata kwala da aka saƙa da hannu aka ɗaura mata a wuya.
ICPC Ta Gano Ma’aikatan Bogi 908 A Wasu Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 50
Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa abubuwan da aka maƙala wa dabbar miyagun ƙwayoyi ne, lamarin da ya sa jami’an suka ƙwace su nan take domin ci gaba da bincike.
Bayan an tabbatar da lafiyar magen, hukumomin suka sake ta, yayin da suke ci gaba da neman mutanen da suka shirya amfani da ita wajen shigar da haramtattun ƙwayoyi cikin gidan yarin.
Lamarin ya jawo hankalin jama’a, domin ya nuna yadda masu aikata laifuka ke ƙirƙiro sabbin dabaru na kauce wa matakan tsaro wajen safarar haramtattun kayayyaki.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
