Connect with us

News

An Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Tsoratar Da Dagaci A Kano 

Published

on

kotu

An gurfanar da Abubakar Isyaku da Aliyu Abdullahi a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jaba, Kano, bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifi da kuma tsoratar da Dagacin Gware na Ƙaramar Hukumar Wudil.

Mutanen biyu sun musanta zargin da ake yi musu a gaban kotun da Alkali Malam Mubarak ke jagoranta.

Dakarun Soji Sun Kuɓutar Da Mutane 23  Da Aka Yi Garkuwa Da Su A  Zamfara

Lauyar Aliyu, Barista Sahura Aliyu Abdullahi, ta nemi a ba shi beli, inda kotun ta amince da buƙatar bisa sharadin cewa ɗan uwansa da mai unguwarsa su tsaya masa.

Kotun ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 21 ga Satumba, 2026.

Lauyar ta kuma bayyana cewa a baya Dagacin ya taɓa shigar da irin wannan ƙara a Kotun Majistare, amma daga bisani ya janye ta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending