Connect with us

News

Za A Saki Wadanda Ba Su Da Laifi Da Hannu A Yunkurin Juyin Mulki —Ministan Tsaron Najeriya

Published

on

615452016 871472428988112 4496895486938445823 n

Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce za a saki mutanen da aka kama bisa zargin hannu a wani shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, idan bincike ya nuna cewa ba su da laifi.

Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Channels Television, inda ya ce hukumomin tsaro suna gudanar da bincike domin tabbatar da cewa ba a hukunta mutanen da ba su da hannu a lamarin ba.

Sarkin Yauri Ya Yaba Wa Gwamna Nasir Idris Bisa Ayyukan Ci Gaba A Masarautar

Ya ce wadanda aka tabbatar da cewa su ne manyan masu ruwa da tsaki a shirin ne kawai za a gurfanar da su gaban kotu.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa zargin yunkurin juyin mulkin na gaskiya ne, yana mai cewa wadanda ake zargin sun yi niyyar aiwatar da shi. Ya ce DSS da NIA na ci gaba da bincike, yayin da wasu daga cikin wadanda aka kama tuni aka gurfanar da su a kotu.

An fara samun labarin zargin shirin juyin mulkin ne a shekarar 2025, bayan da aka kama wasu manyan jami’an soji bisa zargin karya dokokin aikin soja. Daga baya gwamnati ta shigar da kara kan wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin, da laifukan cin amanar kasa, ta’addanci da kuma safarar kudaden tallafa wa ta’addanci.

Advertisement

Musa ya bukaci ‘yan Najeriya su kare dimokuradiyya tare da magance matsalolin kasar ta hanyoyin dimokuradiyya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending