News
Sarkin Yauri Ya Yaba Wa Gwamna Nasir Idris Bisa Ayyukan Ci Gaba A Masarautar
Daga Khadijat Saidu Kabiru
Sarkin Yauri, Dr. Zayyanu Abdullahi, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Kwarada Dr. Nasir Idris, bisa ayyukan ci gaba da gwamnatin sa ta yi a Masarautar Yauri, musamman a fannin tsaro, ilimi, lafiya da noma.
Sarkin ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin da Kungiyar Kafafen Yada Labaran Jihar Kebbi, karkashin jagorancin Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, suka kai masa ziyar girmamawa a fadarsa dake Yauri.
Wasu Iyayen Na Da Hannu Wajen Fadan Daba A Wasu Unguwannin Kano – CP Bakori
Dr. Zayyanu ya yabawa gwamnan bisa jajircewarsa wajen kai ziyara yankunan da ‘yan bindiga suka mamaye kafin ya hau mulki da kuma bayan ya hau mulki. A cewarsa, hakan ya kai ga tura jami’an tsaro wanda ya mayar da zaman lafiya kuma ya sa manoma suka dawo gonakinsu.
“Ya zo da kansa ya shiga cikin wannan daji tare da su. Ya ce tun da aka ba shi amanar, dole ne ya tabbatar da an dawo da zaman lafiya da tsaro. Muna godiya matuka,” in ji Sarkin.
Sarkin ya kuma lissafa wasu ayyukan gwamnati a masarautar, wadanda suka hada da gyara da habaka *Babban Asibitin Yauri*, gina da gyara makarantu, bai wa ‘yan matan da ‘yan bindiga suka sace tallafin karatu, bai wa manoma kayan aikin noma da taki, da kuma kafa kasuwar kifi ta zamani a Yauri.
Ya kara yaba wa gwamnan bisa tallafawa masarautar gargajiya, inda ya ce gwamnati ta gyara fadar Sarkin Yauri da kudi har *Naira miliyan 100* sannan ta samar da motoci na gwamnati domin saukaka aiki.
“Wanda ya tsaya da Yauri, Yauri za ta tsaya da shi. Gwamna ya tsaya da mu, dole ne mu mayar masa. Muna yi masa addu’a Allah ya ci gaba da shiryarwa da karewa da bashi nasara,” in ji shi.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yada Labarai, Alhaji Yakubu Ahmed ya ce gwamnatin Nasir Idris ta samu nasarori da dama cikin shekaru 2 kacal.
Ya lissafa gina hanyoyi, daukar malamai 2,000, inganta albashi da walwala ma’aikata, da kuma kokarin jan hankalin masu zuba jari a fannin lithium da noma domin samar da ayyukan yi ga matasa.
Ya ce kungiyar ta zo ne domin ganin ayyukan gwamnati da kuma isar da saqo ga jama’a.
