News
Mutane Uku Sun Mutu Yayin Da Wata Mota Ta Fado Daga Gadar Da Ke Kan Titin Lagos Zuwa Ibadan
Mutane uku sun mutu, yayin da wasu 10 suka samu raunuka bayan wata mota ta fado daga gadar Long Bridge da ke kan titin Lagos zuwa Ibadan.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:24 na yammacin Juma’a, a kusa da Mikano, a hanyar zuwa Legas.
Dakarun Soji Sun Tarwatsa Ɗaliban Jami’ar AAUA Da Suke Gudanar Da Zanga-zanga
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa.
Ya ce motoci uku ne suka yi hatsarin, inda mutum 16 ke cikinsu. Maza 12 da mata huɗu ne abin ya shafa, yayin da mata uku suka rasa rayukansu.
Akinbiyi ya ce tsananin gudu da rashin iya sarrafa abin hawa ne suka haddasa hatsarin.
Ya ce jami’an TRACE, FRSC, ’yan sanda da jami’an agajin gaggawa sun isa wurin, inda aka kwashe wadanda suka samu raunuka zuwa asibitoci domin samun kulawa.
Ya ƙara da cewa an kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa dakunan ajiye gawarwaki, yayin da aka kwashe motocin da hatsarin ya shafa zuwa tashar ’yan sanda ta Warewa domin ƙarin bincike.
Hatsarin ya kuma ɗan kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa, amma daga bisani aka dawo da zirga-zirga yadda ya kamata.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
