Connect with us

News

Rajistar Masu Zabe: Kano Na Kan Gaba, Waiya Ya Fadada Gangamin PVC

Published

on

20260614 194325 COLLAGE

Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Jama’a Kan Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya sanar da kafa kwamitoci 12 na musamman domin ƙara kaimi wajen wayar da kan jama’a su yi rajistar zaɓe tare da karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC).

Waiya ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da kwamitocin, inda ya ce matakin ya zama dole domin ci gaba da riƙe matsayin da Kano ke da shi na kan gaba a ƙasar nan wajen yawan masu yin rajista a ƙarƙashin shirin Rajistar Masu Zaɓe Ta Kullum (CVR) na Hukumar INEC.

Advertisement

Ya ce an tsara kwamitocin ne domin isa ga kowane ɓangare na al’umma, tare da tabbatar da cewa saƙon rajistar zaɓe da muhimmancin karɓar PVC ya kai ga jama’a har zuwa matakin ƙauyuka da unguwanni.

Sabbin kwamitocin sun haɗa da wakilai daga gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai, ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin ƙwadago, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki.

Advertisement

A cewarsa, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Alhaji Muhammad Tajo Othman, ne zai jagoranci kwamitin hulɗa da ƙananan hukumomi, yayin da Kwamishinan Raya Dabbobi, Dakta Aliyu Isa Aliyu, zai shugabanci kwamitin nazarin bayanai da fasahar sadarwa.

Hajiya Amina Abdullahi za ta jagoranci ɓangaren wayar da kan mata, yayin da Manajan Daraktan Radio Kano, Abubakar Adamu Rano, zai jagoranci kwamitin yaɗa labarai.

Advertisement

Haka kuma, Dan Malikin Kano kuma Hakimin Rimin Gado, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai, zai kula da hulɗa da sarakunan gargajiya, yayin da Malam Ibrahim Abubakar Tofa, Sakataren Majalisar Malamai ta Kano, zai jagoranci hulɗa da malamai da ƙungiyoyin addini.

Sauran kwamitocin sun haɗa da na hulɗa da ’yan kasuwa, ƙungiyoyin sufuri, ɗalibai, ƙungiyoyin fararen hula, jam’iyyun siyasa, masu buƙata ta musamman, Fulani da kuma ƙungiyoyin ƙwadago.

Advertisement

Da yake jawabi a wajen taron, Waiya ya ce an zaɓi shugabannin kwamitocin ne bisa cancanta da ƙwarewa domin tabbatar da cewa an samu tasiri a kowane mataki.

Ya jaddada cewa aikin kwamitin bai tsaya kan rajistar masu zaɓe kawai ba, har ma ya haɗa da ƙarfafa wa jama’a gwiwar karɓar katin zaɓensu da kuma fitowa domin kaɗa ƙuri’a lokacin zaɓe.

Advertisement

“Ba wai rajista kawai muke son mutane su yi ba. Muna son su karɓi katin zaɓensu kuma su yi amfani da shi wajen zaɓen shugabannin da suke ganin za su kawo ci gaba. Hakan ne zai ƙarfafa dimokuraɗiyya,” in ji Waiya.

Ya kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da gwamnatin jihar ke bayarwa wajen tabbatar da nasarar wannan gangami.

Advertisement

Waiya ya ce kafa waɗannan kwamitoci wata hanya ce ta tabbatar da cewa babu wani ɓangare na al’umma da aka bari a baya a ƙoƙarin ƙara yawan masu rajistar zaɓe da masu shiga harkokin dimokuraɗiyya a Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending