Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Dakatar Da Shugabar  KNUPDA

Published

on

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya dakatar da Babbar Darakta a Hukumar Tsara Muhallai da Ci gaba ta Jihar Kano (KNUPDA) Arc. Hauwa Hassan Tudun-wada a matsayin wani bangare na kokarin magance matsalar da ake zargin tafkawa a harkokin gudanar da tsare-tsare da ci gaban birane a fadin jihar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Kano ke kara tsananta matakan dakile gine-gine ba bisa ka’ida ba da sauya filaye ba bisa ka’ida ba da kuma karya dokokin tsare-tsaren birane a sassa daban-daban na birnin Kano.

Advertisement

A cewar mai taimaka wa Gwamna Yusuf kan harkokin yada labarai, Nanu Kankarofi, gwamnatin jihar, ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ta kafa wani kwamiti mai karfin iko don duba batutuwan da suka shafi keta dokokin tsare-tsaren birnin da ayyukan KNUPDA.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar da ke tattara bayanai na Labarin Kasa ta Kano (KANGIS), Dr. Dalhatu Aliyu Sani, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Aiki na Musamman na Jihar Kano kan Tsarin Gidaje.

Advertisement

Shima Musa Tanko Muhammad, sakataren yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa da aka bai wa dan jarida ya tabbatar da dakatarwar.

“A matsayin wani bangare na matakan tabbatar da gaskiya da kuma sauƙaƙe bincike ba tare da wata matsala ba, Gwamna ya umarci Manajan Darakta ta KNUPDA da Daraktan Gine-gine na Hukumar da su sauka daga kan mulki har tsawon lokacin binciken,” in ji Musa Garba.

Advertisement

An dai dauki wannan mataki ne na dakatarwar da aka yi da kuma kafa kwamitin bincike a matsayin wani kokari na gyare-gyare da nufin dawo da da’a, rikon amana da kuma gaskiya a fannin tsare-tsare na jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending