News
Kar A Dogara Da Bashi, A Fara Samar da Ayyukan Yi — Okonjo-Iweala Ta Shawarci Shugaba Tinubu
Babbar Daraktar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta gargaɗi gwamnatin Tarraya da ta shiga taitayinta wajen ciye-ciyen bashi, ta kuma ce dole ne tsare-tsaren tattalin arziƙi su bunƙasa rayuwar ƴan ƙasa.
Ta kuma yi kira ga gwamnatin ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da ta bijiro da su, tare da samar da ayyukan yi da haɓaka tattalin arziƙi domin bunƙasa rayuwar matasa.
Kotu Ta Yanke Wa Amarya Hukuncin Kisa Kan Hallaka Mijinta Kwana 9 Bayan Aure A Kano
Ngozi ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, a wajen wani taron kasuwanci na nahiyar Afirka da ya gudana a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ta kuma ce ba wai za a dubi nasarar Najeriya ne kawai da ci gaban da aka samu kan wasu alamun tattalin arziƙi ba, a maimakon haka dole ne Najeriya a samu kyakkyawan yanayin rayuwa ta hanyar ayyukan yi da damarmaki.
Okonjo ta ce Najeriya ƙasa ce mai tarin matasa da kullum su ke fafutukar inganta rayuwarsu, sai dai ba sa samun ayyukan yi saboda shi ne babbar matsalar da ake fuskanta a ƙasar.
Tun bayan zuwan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2023, gwamnatinsa ta janye tallafin man fetir tare da sauran tsare-tsaren tattalin arziƙi.
Sai dai ƙudurce-ƙudurcen sun janyo matsin rayuwa, inda da yawan ƴan ƙasa ke fuskantar tsadar kayan abinci, zirga-zirga, da sauran abubuwa masu muhimmanci.
