News
INEC: ’Yan Sanda Su Ne Ya Kamata Su Jagoranci Ba Da Tsaro Lokacin Zaɓe, Ba Sojoji Ba
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa bai kamata a riƙa tura dakarun sojoji domin kula da tsaro a lokacin gudanar da zaɓe ba, face idan yanayin tsaro ya taɓarɓare har ya zama dole su shiga domin tallafa wa hukumomin tsaro na farar hula.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan a ranar Alhamis ta bakin Daraktan Harkokin Shari’a na hukumar, Al-Hassan Umar, yayin wani taro da aka gudanar a Kwalejin Yaƙi ta Sojojin Ƙasa da ke Abuja.
An Cafke Wani Bisa Zargin Yunƙurin Satar Adaidaita Sahu A Kano
Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace rawar da kowace hukuma ke takawa wajen gudanar da zaɓe, inda ya jaddada cewa Hukumar ’Yan Sandan Najeriya ce ke da alhakin jagorantar ayyukan tsaro a lokacin zaɓe.
Amupitan ya ce amfani da sojoji a lokacin zaɓe bai kamata ya zama al’ada ba, domin ana kiran su ne kawai idan akwai wata babbar barazana ga tsaro da jami’an tsaron farar hula ba za su iya shawo kanta su kaɗai ba.
“A matsayina na masanin shari’a, ina sake jaddada cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadi yadda za a gudanar da tsaron zaɓe da kuma nauyin da ya rataya a kan hukumomin da abin ya shafa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bin tanade-tanaden doka da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin INEC da hukumomin tsaro zai taimaka wajen gudanar da zaɓe cikin lumana, adalci da sahihanci, tare da ƙarfafa amincewar al’umma ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
