News
Dakarun Soji Sun Hallaka Babban Jami’in Yada Farfagandar ISWAP Abu Salim Al-Barnawi
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun nuna cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun hallaka Abu Salim Al-Barnawi, wanda ake zargi da kasancewa ɗaya daga cikin manyan jami’an yaɗa farfagandar ƙungiyar ISWAP.
A cewar bayanan tsaro, Abu Salim ya kasance cikin manyan mutanen da ke da alhakin ɗaukar hotuna da bidiyoyin hare-haren da ƙungiyar ke kaiwa, tare da amfani da su wajen yaɗa manufofin ƙungiyar da kuma jan hankalin sababbin mambobi.
Gwamnatin Tarayya Za Ta Bai Wa Matasa Bashin Laptop
Majiyoyin sun ce ya mutu ne a makon da ya gabata yayin wani yunƙurin kai hari kan sansanin sojojin Najeriya, sai dai harin bai cimma nasara ba bayan dakarun suka mayar da martani mai ƙarfi.
Rahotannin sun kuma nuna cewa kafin mutuwarsa, Abu Salim Al-Barnawi ya jagoranci hare-hare da dama a yankunan da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda ya kasance cikin manyan jagororin ayyukan ƙungiyar a yankin.
Masana harkokin tsaro sun bayyana mutuwarsa a matsayin babbar koma baya ga ISWAP, musamman ta fuskar yaɗa farfaganda da ɗaukar sabbin mayaƙa, yayin da dakarun sojin Najeriya ke ci gaba da ƙara matsin lamba kan ƙungiyar a yankin Arewa maso Gabas.
Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da mutuwar Abu Salim Al-Barnawi ba.
-
Opinion3 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion3 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News7 days ago
An Sace Shugaban Makaranta Da Dalibai Masu Rubuta Jarabawar NECO A Kogi
