News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Bai Wa Matasa Bashin Laptop
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shiri na bai wa matasa damar samun kwamfutocin tafi-da-gidanka (Laptop) ta hanyar bashi mai sauƙin biya, domin ƙara musu damar cin gajiyar tattalin arzikin zamani.
Shirin, wanda Hukumar Bayar da Lamuni ta Ƙasa (CREDICORP) ta ƙaddamar tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani ta Tarayya, an sanya masa suna Credit for Laptops, Internet, Connectivity and Knowledge Digital Devices (C.L.I.C.K.D.).
Jihohi 17 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa — Gwamnatin Tarayya
A matakin farko, shirin zai samar da laptop 1,000 da aka haɗa a Najeriya ga waɗanda suka cancanta daga cikin mahalarta shirin horas da matasa kan fasahar zamani na Gwamnatin Tarayya, wato Three Million Technical Talent (3MTT), ta hanyar dandalin Learn2Earn.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin a Abuja, Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani, ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa matasan Najeriya ba wai sun samu horo kan fasahar zamani kaɗai ba, har ma sun mallaki kayan aikin da za su taimaka musu wajen amfani da ilimin da suka koya.
A cewarsa, samar da damar mallakar kwamfuta ta hanyar bashi zai taimaka wa matasa wajen samun ayyukan yi, gudanar da kasuwanci ta intanet da kuma ƙara yawan masu shiga tattalin arzikin dijital na ƙasar.
-
News4 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News5 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News7 days ago
“Wasu Daga Cikin Mutanen Da Buhari Ya Amince Da Su Ne Suka Ci Amanarsa” — Lawal Daura
