Connect with us

News

’Yan Sanda Sun Kama Mutum 262, Sun Ceto 27 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Cikin Mako Guda

Published

on

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce jami’anta sun kama mutane 262 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da kuɓutar da mutane 27 da aka yi garkuwa da su cikin mako guda.

Rundunar ta ce an samu nasarorin ne a ayyukan da jami’anta suka gudanar a faɗin ƙasar tsakanin ranar 5 zuwa 11 ga Satumba, 2026.

Zanga-zanga Ta Barke Kan Karin Kudin Man Fetur A Syria

A cikin sanarwar da CSP Aniete Iniedu ya fitar, rundunar ta ce ta kwato bindigogi 34, harsasai 375 da motoci 11. Haka kuma, an kashe mutane 11 da ake zargi ’yan bindiga ne yayin samamen.

Waɗanda aka kama ana zarginsu da laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, zama ’yan bindiga da ƙungiyoyin asiri, da safarar mutane da miyagun ƙwayoyi.

Rundunar ta ce a cikin wannan lokacin ta samu rahotannin kisan kai 50, fashi da makami 28, garkuwa da mutane 27 da hare-haren ’yan bindiga 22

Advertisement

A Delta, jami’an ’yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 60 da aka yi garkuwa da shi bayan musayar wuta da masu garkuwa da mutanen.

A Sokoto kuwa, an kashe mutane huɗu da ake zargi ’yan bindiga ne yayin wani samame, inda aka kwato bindigar AK-47 da harsasai 28.

A Kaduna, jami’an tsaro tare da ’yan sa-kai da mafarauta sun ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su, tare da kashe wasu mutane biyu da ake zargi ’yan bindiga ne. Sai dai mafarauta uku sun rasa rayukansu, yayin da wani ya samu rauni.

A Akwa Ibom kuma, jami’an tsaro sun dakile wani shirin yin garkuwa da mutane tare da kwato bindiga, harsasai da kwale-kwale biyu.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike da kuma ƙoƙarin kama sauran waɗanda ake zargi.

 

Advertisement

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending