News
An Rufe Rassan Bankuna 476 Sakamakon Tabarbarewar Tattalin Arziki — Rahoto
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce an rufe ko dakatar da ayyukan rassan bankuna da cibiyoyin hada-hadar tsabar kuɗi 476 a faɗin ƙasar tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025.
Bayanan da ke cikin 2025 Statistical Bulletin na CBN sun nuna cewa yawan rassan bankuna da cibiyoyin tsabar kuɗi ya ragu daga 5,410 a shekarar 2022 zuwa 4,934 a shekarar 2025.
Ta’adda Sun Bude Wuta Kan Fasinjoji A Cikin Wata Motar Haya A Jos
Wannan ya nuna raguwar kashi 8.8 cikin 100 na wuraren da bankuna ke gudanar da ayyukansu a cikin shekaru ukun.
Binciken ya nuna cewa an samu raguwar rassa 37 a shekarar 2023, sannan 229 a 2024, yayin da aka sake rufe wasu 210 a shekarar 2025.
Hakan na nufin kusan kashi 92 cikin 100 na jimillar raguwar rassan da aka samu a lokacin ta faru ne cikin shekaru biyu na ƙarshe.
Bayanan da CBN da Hukumar Inshorar Adibas ta Najeriya (NDIC) suka tattara sun shafi rassan bankunan kasuwanci, bankunan ’yan kasuwa da kuma bankunan da ba sa amfani da ruwa.
A gefe guda, adadin bankunan da ke aiki a Najeriya ya karu daga 32 a 2022 zuwa 35 a 2024, kafin ya ragu zuwa 34 a 2025. Yawan rassan bankunan Najeriya da ke wajen ƙasar kuwa bai sauya ba, inda suka ci gaba da kasancewa biyu a duk tsawon lokacin.
