Connect with us

News

SAUYIN YANAYI: KWEP Ta Horas Da Mata Kan Kare Muhalli A Kano

Published

on

IMG 20260914 WA0011

Ƙungiyar Mata Masu kula da Muhalli ta Jahar kano (KWEP) ta shirya taron farko na wayar da kan mata kan muhalli, domin ƙara musu ilimi kan kare muhalli da hanyoyin raya muhalli a Jihar Kano.

An gudanar da taron a Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu ta Dake Jahar Kano (KHAIRUN), inda aka tattauna kan sauyin yanayi da yadda mata za su taka rawa wajen magance matsalolin muhalli a cikin al’ummominsu.

Ta’adda Sun Bude Wuta Kan Fasinjoji A Cikin Wata Motar Haya A Jos

Da yake jawabi, Daraktan Sauyin Yanayi na Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jahar Kano, Umar Sale Anka, wanda ya wakilci Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ya ce sauyin yanayi na da matuƙar illa ga mata ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki.

Anka ya Cigaba da cewa Tsfatar muhalli alhaki ne a kan kowa , inda ya buƙaci mata su riƙa kula da muhalli tare da koya wa ’ya’yansu tsaftar muhalli. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na raba itatuwan dasawa tare da horas da mata yadda za su dasa su tare da basu kulawa.

A nata jawabin, Shugabar Kungiyar Mata Masu kula da Muhalli ta Jahar kano KWEP, Hajiya Bara’atu Gwadebe, ta ce an shirya taron ne saboda mata na daga cikin waɗanda matsalolin muhalli suka fi shafa. Ta ce an shirya taron ne domin raba wa mahalarta Taron itatuwan dasawa tare da koya musu yadda za su kula da su, musamman domin yaƙi da hamadar ƙasa.

Advertisement

WakiliyarMu Safiya Muhammad Usman ta Rawaito mana cewa Shugabar Ƙungiyar Mata Yan Jarida ta Kasa (NAWOJ), reshen Kano, Bahija Malam Kabara, ta yi kira ga mata da su guji zubar da shara a magudanan ruwa, inda tace hakan na iya toshe magudanan ruwa tare da ƙara haɗarin ambaliya a lokacin damina.

Taken taron shi ne wayar da kan Mata Domin Kula da Muhalli Mai Ɗorewa a Jihar Kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending