News
Zanga-zanga Ta Barke Kan Karin Kudin Man Fetur A Syria
Zanga-zanga ta barke a sassan kasar Syria bayan da gwamnatin kasar ta sanar da karin kudin man fetur.
Masu zanga-zangar sun tare manyan titunan inda suke ta kona tayoyi na tsawon sa’o’i a yayin da karin farashin man ya haifar da muhawara a kafofin sada zumunta.
SAUYIN YANAYI: KWEP Ta Horas Da Mata Kan Kare Muhalli A Kano
A ranar Lahadi gwamnatin kasar ta sanar da karin farashin litar man fetur da kashi 40 cikin 100 da kuma karin kashi 20 a farashin man dizel.
Gwamnatin ta bayyana karin farashin a matsayin matakin wucin gadi, a sakamakon tashin gwauron zabon farashin mai a kasuwar duniya.
Ta bayyana cewa karin yana kuma da alaka da muhimman gyare-gyare da take yi a matatar mai ta Baniyas, wanda zai kara karfin matatar daga tace gangar mai dubu tamanin a kowance rana zuwa tace ganga dubu dari da talatin a kowace rana.
Karin farashin ya haddasa bore da kone-kone a yankunann Hama da Khan Sheikhoun da Maarat al-Numan inda mutane suka yi ta kone-konen tayoyi a kan tituna.
Ministan Mai na kasar, Mohammed al-Bashir ya sanar a ranar Asabar cewa, a halin yanzu kasar tana tace gana dubu dari da biyu na danyen mai a kullum, alhali tana bukatar ganga dubu dari uku da ashirin da biyar a kowace ranar a cikin gida, lamarin da ya sa taka shigo da wani kawo na man daga kasashen waje comin cike gibin, kamar yadda
A cewarsa, ma’aikatar za ta rika lura da yanayin farashin mai a kasuwar duniya tare da yin aiki na tsawon lokaci domin cike gibin bukatar mai na cikin gida a kasar.
Man fetur na kasar Syria yana da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Syria, a yayin da kasar ke kokarin farfadowa bayan yakin basasa na shekara 14.
