News
Ta’adda Sun Bude Wuta Kan Fasinjoji A Cikin Wata Motar Haya A Jos
Ana fargabar akalla mutum tara sun bakunci lahira bayan ’yan ta’adda sun bude wuta kan fasinjoji a cikin wata motar haya a mahadar Dungus Junction dake yankin Kuuru a Karamar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato.
Shaidu sun bayyana wa wakilinmu cewa ’yan bindiga sun bude wa motar da ke hanyar zuwa Jos wuta ne bayan da direban ya tsaya a wurin domin sauke wasu fasinjoji.
Matatar Dangote Za Ta Buɗe Sayar Da Hannayen-Jari Na Naira Tiriliyan 2.15
Sun kara da cewa maharan sun yi raga-raga da motar da harbin bindiga a yayin da aka ga jini na malala.
Wani makwabci kuma malamin daya daga cikin fasinjojin da aka kashe, Lawan Suleimna ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan an tsayar da motar a mahadar.
“Direban motar dalibina ne, mutum uku daga cikinsu daga yankinmu, Bukuru, suke, kuma an ka gawarwakinsu asibiti. ’Yan uwansu na kokarin karbar gawarwakin domin a yi musu jana’iza,” in ji Malam Sulaiman.
Kakakin Kungiyar Matasa na Kabilar Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabab
Kakakin Kungiyar Matasa na Kabilar Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya bayyana cewa, “Abin ya faru ne da misalin karfe 9.40 na dare. Mutanen da ’yan ta’addan suka kashe fasinjojiji ne da ke kan hanayar su ta zuwa Jos. Daga cikin mutanen da aka kashe har da wani jami’in rudunar Operation Rainbow. Abin ban takaici ne matuka.”
Ya bayyana cewa wasu daga cikin fasinjojin sun samu raunuka, aka garzaya da su asibiti, inda daga bisani wasu daga cikinsu suka rasu.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ba ta kai ga fitar da sanarwa ko yin tsokaci game da lamarin ba, har zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoto.
