News
Jirgin shahararren mawaki Ya Kauce Hanya, Ya Kama da Wuta A Brazil
Wani ƙaramin jirgin sama da ke ɗauke da shahararren mawakin Brazil, Rey Vaqueiro, da wasu mutane bakwai ya kauce daga titin saukar jiragen sama tare da kama da wuta a filin jirgin saman Parelhas da ke jihar Rio Grande do Norte.
Lamarin ya faru da sanyin safiyar Lahadi, 13 ga Satumba, lokacin da jirgin kirar Cessna 550 Citation Bravo, mai lambar rajista PP-WMO, ke ƙoƙarin sauka a filin jirgin.
NDLEA Ta Kama Matashi Mai Shekaru 20 Da Kwayoyin Pregabalin 785,000 a Kano
Rahotanni sun ce jirgin ya wuce ƙarshen titin saukar kafin daga bisani wuta ta kama shi, inda injinan jirgin biyu suka kama da wuta. Jami’an kashe gobara sun kwashe kusan sa’o’i biyar suna aikin kashe gobarar.
Jirgin na ɗauke da mutane takwas, ciki har da fasinjoji shida da ma’aikatan jirgin biyu. Rahotanni sun ce dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun samu damar fita kafin wutar ta mamaye shi.
Sai dai wasu daga cikinsu sun samu ƙananan raunuka, amma babu rahoton wani da ya mutu ko ya samu mummunan rauni sakamakon hatsarin.
Wutar ta lalata jirgin gaba ɗaya, yayin da hukumomin Brazil suka fara bincike domin gano musabbabin hatsarin. Cibiyar Bincike da Kare Hadurran Jiragen Sama ta Brazil, CENIPA, ce ke jagorantar binciken, yayin da har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa jirgin ya tsallake titin saukar ba.
