Connect with us

News

Farashin kayan Miya Ya Karye Da Kaso 60 Cikin 100 A Kano

Published

on

kayan miya (1)

Farashin kayan Miya ya ragu sosai a wasu kasuwannin Jihar Kano, sakamakon karuwar kayan amfanin gona da manoma ke kawo wa kasuwanni.

Wani binciken Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a kasuwannin Yankaba, kasuwar Titin Gwarzo da wasu sassan birnin Kano, ya gano cewa farashin ƙaramin kwandon tumatir ya sauka daga N10,000 zuwa N4,000, wanda ke nuna raguwar kusan kashi 60 cikin 100.

NDLEA Ta Kama Matashi Mai Shekaru 20 Da Kwayoyin Pregabalin 785,000 a Kano

Haka kuma, farashin barkono ya ragu daga N9,000 zuwa N4,000, yayin da farashin attarugu ya sauka daga N10,000 zuwa N4,000.

Wani ɗan kasuwa a Kano, Malam Musa Isyaku, ya ce ana sa ran farashin kayan lambun zai ci gaba da saukowa har zuwa ƙarshen damina, saboda yawan kayan amfanin gona da ake kawo wa kasuwanni.

Sai dai ya ce rashin isassun wuraren adana kayan lambu na ci gaba da zama babban ƙalubale ga ’yan kasuwa, musamman masu sayar da tumatir, saboda kayan na saurin lalacewa sakamakon zafi da sauyin yanayi.

Advertisement

Malam Isyaku ya yi kira ga gwamnati da ta samar da ƙarin wuraren adana kayan lambu, musamman masu amfani da na’urorin sanyaya kaya, domin rage asarar amfanin gona.

Ya kuma roƙi kamfanoni masu zaman kansu da su saka jari wajen samar da ƙananan wuraren adana tare da sarrafa kayan lambu, domin taimaka wa manoma da ’yan kasuwa wajen rage asarar amfanin gona da kuma tabbatar da samun kayan a duk shekara.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending