News
Jihohi 17 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa — Gwamnatin Tarayya
Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) ta yi gargaɗin cewa jihohi 17 na Najeriya na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa tsakanin ranar 21 zuwa 27 ga watan Yulin 2026.
Hukumar ta ce hakan na zuwa ne bayan da wasu manyan koguna da madatsun ruwa suka tumbatsa, lamarin da ka iya haddasa ambaliya a yankuna da dama.
Kotu Ta Daure Mutune 12 Kan Wulakanta Takardun Naira
Babban Daraktan NIHSA, Umar Ibrahim Mohammed, ya ce binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa Kogin Karam da Madatsar Waya da kuma Kogin Amber sun cika maƙil, saboda haka ake ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki.
A cewarsa, jihohin da ke cikin haɗarin sun haɗa da Bauchi, Edo, Imo, Kaduna, Filato da Benue, tare da wasu jihohi 11.
Rahoton hukumar ya nuna cewa Jihar Bauchi ce ke fuskantar barazana mafi girma, inda ake hasashen ambaliyar za ta shafi garuruwa 1,841, makarantu 145, cibiyoyin lafiya 101 da kuma kasuwanni takwas.
NIHSA ta buƙaci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da hukumomin agaji na jihohi, ƙananan hukumomi da shugabannin al’umma su fara kwashe mutane, dabbobi da sauran kayayyaki masu muhimmanci daga yankunan da ke cikin haɗari.
Hukumar ta kuma shawarci mazauna wuraren da aka yi hasashen za su fuskanci ambaliya da su bi umarnin hukumomi tare da ɗaukar matakan kariya domin kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi.
-
News4 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News5 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News7 days ago
“Wasu Daga Cikin Mutanen Da Buhari Ya Amince Da Su Ne Suka Ci Amanarsa” — Lawal Daura
