News
Kotu Ta Daure Mutune 12 Kan Wulakanta Takardun Naira
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Warri na Jihar Delta, ta yanke wa wasu mutum 12 hukuncin zaman gidan yari bayan kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na Naira.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC ta gurfanar da mutanen a gaban kotun kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X ranar Talata ta bayyana.
NSCDC Ta Gano Jami’ar Bogi Da Ke Karɓar Har Naira Miliyan 1.5 A Legas
EFCC ta gurfanar da su bisa zargin watsa takardun kuɗin Naira yayin wani biki, abin da doka ta haramta.
Mai Shari’a Hyeladzira Nganjiwa ne ya yanke wa mutanen hukunci na zaman gidan gyaran hali na wata 6 ko kuma biyan tarar N150,000 bayan waɗanda ake tuhumar sun amsa laifin da ake zarginsu da shi.
Advertisements
