Connect with us

News

Gwamnatin Sokoto Ta Bayar Da Umarnin Rufe Masallacin Sheikh Musa Lukuwa

Published

on

IMG 20260911 WA0284 768x436

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayar da umarnin rufe masallacin Juma’a na Musa Lukuwa da ke Mabera, a birnin Sakkwato, bayan caka wa malamin Musulunci Sheikh Musa Lukuwa wuƙa da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata da kuma kashe maharin da masu ibada a masallacin suka yi.

Gwamnatin ta kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da ayyana masallacin a matsayin wajen aikata babban laifi har sai an fitar da sanarwa ta gaba.

A Shirye Nake Na Fuskanci Cikakken Bincike Kan Zargin Alaƙa Da ’Yan Bindiga — Sanata Shehu Buba

Umarnin na ɗauke a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata daga ofishin Darakta-Janar kan Kafafen Watsa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnati, Abubakar Bawa.

An rufe masallacin a yayin da ake fuskantar ƙarin tashin hankali a wasu yankunan babban birnin jihar bayan lamarin, wanda ya auku jim kaɗan bayan Lukuwa ya ja Sallar Juma’a a masallacin.

Rahotanni sun ce an yi zargin wani matashi daga cikin masallata da caka wa malamin wuƙa sau biyu a wuya. Sauran masu ibada sun far wa maharin tare da kashe shi.

Advertisement

‘Yansanda sun tabbatar da kuɓutar da Lukuwa bayan harin kuma an kai shi Asibitin Ƙwararru na Sakkwato don duba lafiyarsa.

Kakakin ‘yansandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, daga bisani ya bayyana cewa an sallami malamin bayan an yi masa magani a ciwon da ya samu a wuya da hannun hagu.

An rawaito cewa lamarin ya janyo zanga-zanga da tsanantar tashin hankali a yankunan da suka haɗa da Sahara, Bello Way da Aliyu Jodi, inda wasu masu kasuwanci suka rufe na wucin-gadi, a yayin da jami’an tsaro kuma suka bazu a wurare masu muhimmanci don hana ɓarkewar rikici da karya doka.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending