News
“Wasu Daga Cikin Mutanen Da Buhari Ya Amince Da Su Ne Suka Ci Amanarsa” — Lawal Daura
Tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Lawal Daura, ya ce wasu daga cikin mutanen da marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da su a gwamnatinsa sun ci amanarsa.
Daura ya ce matsalolin da gwamnatin Buhari ta fuskanta sun samo asali ne, a wasu lokuta, daga yadda shugaban ya dogara da mutanen da ya amince da su wajen gudanar da muhimman ayyuka.
Wani Tsoho Mai Shekaru 87 Ya Yanke Hannun Alkali Da Adda A Adamawa
Ya bayyana wasu daga cikin waɗannan mutanen a matsayin “’yan amshin shata”, yana mai cewa sun gaza sauke nauyin amanar da aka ba su.
Daura ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Television ranar Litinin.
Ya ce lamarin ya nuna illar dogaro da kusanci ko amincewar mutum kawai wajen naɗa jami’an gwamnati, maimakon a duba ƙwarewa da cancantar mutum.
“Na san abin da wasu daga cikinsu suka aikata, kuma na san cikakkun bayanai kan abubuwan da suka faru,” in ji shi.
‘Babu Cabal a Gwamnatin Buhari’
Daura ya kuma musanta zargin cewa yana cikin wata ƙungiyar masu hana ruwa gudu, wato cabal, da ake zargin ta yi tasiri wajen samun damar ganawa da Buhari ko kuma shafar shawarwari da yanke hukunci a gwamnatin.
Ya ce kasancewarsa kusa da Buhari ya samo asali ne daga nauyin aikinsa na Darakta-Janar na DSS.
“Babu cabal,” in ji Daura, yana mai cewa kasancewarsa kusa da shugaban ƙasa ya zama dole ne saboda yanayin aikinsa na leƙen asiri da tsaro.
Daura Ya Kare Gwamnatin Buhari
Daura, wanda ke takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa gwamnatin Buhari ita ce mafi muni a tarihin siyasar Najeriya.
Ya ce masu irin wannan ra’ayi ya kamata su duba abubuwan da suka faru a Najeriya daga shekarar 1995 zuwa lokacin da Buhari ya bar mulki a 2023 kafin su yanke hukunci.
Tsohon shugaban DSS ɗin ya ce ya kasance mai biyayya ga Buhari, kuma ya kare gwamnatinsa a lokacin da yake kan jagorancin hukumar.
Sai dai ya ce abubuwa sun fara lalacewa ne bayan ya bar muƙaminsa a shekarar 2018.
