Connect with us

News

Wani Tsoho Mai Shekaru 87 Ya Yanke Hannun Alkali Da Adda A  Adamawa

Published

on

Octogenarian charged with cutting off Adamawa judges hand 1000x600

Wani dattijo mai shekaru 87, Dahiru Garba, ya gurfana a gaban kotu a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, bisa zargin yanke hannun wani alƙali da adda.

Ana zargin Dahiru da kai wa Alƙali Dauda Hamman, na Kotun Yankin Mayo-Ine da ke Ƙaramar Hukumar Fufore, hari da adda a ranar 31 ga Agusta, 2026, a lokacin da alƙalin ke sauraron wata ƙara da ta shafi wanda ake zargin da wani mutum mai suna Ismail Yusuf.

Wani Tsoho Mai Shekaru 87 Ya Yanke Hannun Alkali Da Adda A  Adamawa

Rahotanni sun ce Dahiru ya ɗauki adda a yayin zaman kotun, inda ya kai wa alƙalin hari tare da yanke masa hannu da kuma jikkata shi.

Bayan faruwar lamarin, ’yan sanda sun kama Dahiru tare da tura batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka, SCID, da ke Yola domin gudanar da bincike.

A ranar 8 ga Satumba, 2026, an gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Majistare ta Ɗaya da ke Yola, ƙarƙashin jagorancin Babban Alƙalin Majistare, Ismail Bello Shelleng.

Advertisement

’Yan sanda sun tuhumi Dahiru da laifin haddasa mummunan rauni, wanda ya saɓa wa Sashe na 219 na Dokar Penal Code ta Jihar Adamawa ta 2018.

Bayan an karanta masa tuhumar kuma aka fassara masa, Dahiru ya amsa laifin. Ya ce “shaiɗan ne ya sa ni”, tare da bayyana nadamarsa kan abin da ya faru.

Kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Yola, yayin da ake jiran ci gaba da sauraron shari’ar.

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending