Connect with us

News

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Basarake Bisa Zargin Kona Wani Mutum Kan Zargin Satar Itacen Girki

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai
Advertisements
ads

Rundunar Ƴansandan Jihar Bayelsa ta tabbatar da kama wani ɗan basarake mai suna Ibobuminate Oweifa, bisa zargin ƙona wani mutum da ake zargin ya yi yunƙurin satar itacen girki a ƙauyen Okodi da ke Ƙaramar Hukumar Ogbia.

Rahotanni sun ce wanda abin ya shafa, Godgift Biko, ya samu munanan raunukan ƙonewa sakamakon harin, kuma a halin yanzu yana karɓar kulawa ta musamman a sashen gaggawa na Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da ke Yenagoa.

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Basarake Bisa Zargin Kona Wani Mutum Kan Zargin Satar Itacen Girki

Kwamishinan Ƴansandan Jihar Bayelsa, Iyamah Edebor, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an rundunar sun yi gaggawar kai ɗauki bayan samun rahoton abin da ya faru.

A cewarsa, jami’in kula da yankin (DPO) ya jagoranci aikin ceto wanda aka kai wa harin, inda aka kai shi wani asibiti domin samun agajin gaggawa kafin daga bisani aka kama wanda ake zargi da aikata laifin.

Kwamishinan ya ƙara da cewa rundunar ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yana mai tabbatar da cewa da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.

Advertisement

 

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending