Connect with us

News

Yadda daliban Jami’ar MAAUN Suka Cira Tuta A Jarabawar Karshe Na Kwararrun A Fannin Kimiyyar Gwaje-gwaje, Suka Yi Nasarar Cin 100 bisa 100

Published

on

FB IMG 1782688771950
Advertisements
ads

Jami’ar Maryam Abacha MAAUN ta sake kafa wani sabon tarihi a fannin ilimi bayan dukkan daliban ta na Kimiyyar Gwaje-gwajen Likitanci (Medical Laboratory Science) da suka rubuta Jarabawar Ƙarshe ta Ƙwararru ta shekarar 2026 sun yi nasara, inda jami’ar ta samu nasarar kashi 100 cikin 100.

Wannan gagarumar nasara ta ƙara tabbatar da matsayin MAAUN a matsayin ɗaya daga cikin jami’o’in da ke ba da ingantaccen ilimi a Najeriya.

KOGI: Ana Zargin Dangin Ɗalibi Sun Kashe Malamar Makaranta Saboda Ta Ladabtar da Shi

Daliban Kimiyyar Gwaje-gwajen Likitanci na rubuta jarabawar ƙwararru sau uku a tsawon karatunsu.

Jarabawar farko ana rubuta ta ne a zangon karatu na biyu na matakin aji na 400 (400 Level), sannan a rubuta jarabawa ta biyu da ta ƙarshe a aji na 500 (500 Level), kamar yadda Majalisar Kula da Kimiyyar Gwaje-gwajen Likitanci ta Najeriya (Medical Laboratory Science Council of Nigeria – MLSCN) ta tanada.

Bisa ga taƙaitaccen sakamakon Jarabawar Ƙarshe ta Ƙwararru ta 2026 da MLSCN ta fitar, dukkan ɗalibai 88 na MAAUN da suka zauna jarabawar sun yi nasara tare da samun maki masu kyau.

Advertisement

Wannan nasara ta zama wani muhimmin ci gaba ga jami’ar, inda ta nuna ingancin koyarwa, tsauraran ƙa’idojin ilimi da kuma ƙwazon ɗalibai da malamansu.

Da yake martani kan sakamakon, Shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, ya taya ɗaliban murna bisa wannan gagarumar nasara, yana mai bayyana ta a matsayin wani abin tarihi.

Ya ce samun nasarar kashi 100 cikin 100 a irin wannan jarabawar ƙwararru mai matuƙar gasa, shaida ce ta ƙudurin jami’ar na samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya masu cikakken ƙwarewa da za su iya yin gogayya a matakin ƙasa da ƙasa.

Farfesa Israr ya kuma yaba wa malaman jami’ar da ma’aikatan Sashen Kimiyyar Gwaje-gwajen Likitanci saboda jajircewarsu wajen horas da ɗaliban, tare da ƙarfafa wa waɗanda suka yi nasarar gwiwa da su ci gaba da riƙo da ƙa’idodin ƙwarewa da ɗa’a yayin da suke shirin bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending