Connect with us

News

‘Masu Buƙata Ta Musamman Ba Za Su Ci Gaba da Jira Ba’ — Ƙungiyoyi Sun Yabawa Waiya, Sun Bukaci A Kaddamar Da Hukumar Kano

Published

on

images (13)
Advertisements
ads

Ƙungiyoyin masu buƙata ta musamman (PWDs) a Jihar Kano sun yaba da irin salon shugabancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, bisa yadda yake tabbatar da bai wa kowa damar shiga cikin harkokin gwamnati ba tare da nuna wariya ba.

Ƙungiyoyin sun ce Waiya ya nuna jajircewa wajen haɗa dukkan masu ruwa da tsaki cikin tattaunawa da aiwatar da manufofin gwamnati, ciki har da masu buƙata ta musamman, domin tabbatar da cewa ana sauraron ra’ayoyinsu da kuma la’akari da muradunsu.

Ganduje Ya Nesanta Kansa Da Rahoton Da Aka Danganta Masa Kan Kudaden Gwamnatin Kano

A cewarsu, irin wannan tsari na shugabanci mai rungumar kowa ya ƙara ƙarfafa gwiwar masu buƙata ta musamman, tare da ba su damar taka rawar gani wajen ci gaban al’umma da jihar baki ɗaya.

Sai dai sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta gaggauta aiwatar da dokar kafa Hukumar Masu Buƙata ta Musamman ta Jihar Kano, tare da fara aikinta cikin gaggawa domin tabbatar da cikakken kare haƙƙoƙi da inganta walwalar wannan ɓangare na al’umma.

Sun bayyana cewa fara aiki da hukumar zai taimaka wajen aiwatar da shirye-shirye da manufofi da suka shafi ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa shigar masu buƙata ta musamman cikin harkokin gwamnati da ci gaban jihar.

Advertisement

Ƙungiyoyin sun kuma bayyana fatansu cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su tabbatar da cikakken shigar masu buƙata ta musamman cikin dukkan shirye-shiryen ci gaba, domin gina al’umma mai adalci da bai wa kowa dama.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending