Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 10 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Jigawa 

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama mutane 10 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da satar shanu, damfara da lalata wayoyin wutar lantarki.

Kamen ya biyo bayan ayyukan leƙen asiri da sintiri da jami’an rundunar suka gudanar a ƙananan hukumomin Taura, Malam Madori, Hadejia, Birniwa, Kirikasamma da Kaugama.

Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano, Waiya Ya Samu Lambar Yabo Ta Ƙasa Kan Ƙwarewar Yaɗa Labarai A Lokutan Rikici ‎

Rundunar ta ce ta kwato motoci biyu, shanu shida, babur guda, tunkiya guda, wayar hannu, dala ta bogi 3,100, wayoyin lantarki da aka lalata, da kuma kuɗi naira miliyan 1.1.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Hussaini Umar, wanda ake zargi da damfarar wani mutum naira miliyan 2.661 da sunan samar masa da dalar Amurka, sannan ya aika masa da takardar shaidar cewar an tura masa naira miliyan 23.57, wadda ba gaskiya ba ce.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike domin cafke sauran waɗanda suka tsere, yayin da za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike.

Advertisement

Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa sintiri da ayyukan leƙen asiri domin dakile aikata laifuka a jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending