News
Wasu ’Yan Fashi Sun Shafe Awanni Shida Suna Cin Abinci A Gidan Da Suka Je Sata
Wasu ’yan fashi da makami sun shafe kusan sa’o’i shida a gidan wani magidanci a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, inda suka ci abinci, suka sha barasa, kafin daga bisani su kwashe kuɗaɗe da wasu kayayyaki suka tsere.
Magidancin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce ’yan fashin sun shiga gidansa ne da daddare, kwanaki uku kacal bayan shi da iyalinsa sun koma sabon gidan.
Kotu Ta Sanya 21 Ga Satumba Domin Sauraron Ƙarar Kalubalantar Takarar Shugaba Tinubu
Bayan sun kutsa cikin gidan, ’yan fashin sun nufi ɗakin girki, inda suka ci abincin da suka samu tare da shan barasar da ke cikin gidan.
Da suka kammala, sun ƙwace wayar magidancin, sannan suka yi amfani da ita wajen tura makudan kuɗaɗe daga asusun bankinsa zuwa wani asusu.
Baya ga kuɗaɗen, ’yan fashin sun kuma tafi da wata ƙaramar mota ƙirar Hyundai Santa Fe.
Rahotanni sun ce ’yan sanda sun kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi da aikata fashin, inda biyu daga cikinsu suka amsa laifinsu a yayin bincike.
Waɗanda ake zargin sun bayyana cewa an kama su ne yayin da suke amfani da wasu daga cikin kayayyakin da suka sato a hare-haren da suka kai a sassan Ibadan.
Sun kuma bayyana cewa wani daga cikin ƙungiyar, wanda ya san gidan sosai, shi ne ya jagorance su wajen shiga gidan ta hanyar tsallake katanga.
A cewar waɗanda ake zargin, sun shiga gidan ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, kuma suka kammala ayyukansu da misalin ƙarfe 5:30 na safiya.
Sun kuma amsa cewa sun kai wasu hare-hare a unguwannin Alakia da Oluwo da ke Ibadan, inda suka ƙwace wayoyin mutane tare da karkatar da kusan Naira miliyan 1.5 daga asusun bankunan wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, DSP Ayanlade Olayinka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai ya ce waɗanda ake zargin sun musanta zargin cewa sun yi wa iyalan magidancin fyaɗe.
Rundunar ’yan sandan ta ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a fashin.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
