Connect with us

News

Farfesoshi Da Alkalai Na Taimakawa Wajen Magudin Zaɓe — Peter Obi

Published

on

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya zargi wasu farfesoshi da hannu wajen taimaka wa wasu mutane yin magudin zaɓe a Najeriya.

Obi ya bayyana hakan ne a wajen taron tattaunawa kan dimokuraɗiyya da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a jihar Bauchi, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ƙwararru ke taimakawa wajen raunana tsarin zaɓe a ƙasar.

Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa  —NiMet

Ya kuma zargi wasu alkalai da nuna son kai, yana mai cewa wasu daga cikinsu na nuna biyayya ga jam’iyyar da ke mulki, lamarin da ya ce na iya rage amincewar jama’a ga bangaren shari’a da tsarin zaɓe.

Haka kuma, Obi ya soki ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa kan matakin cire jabun takardu daga cikin laifukan da suka shafi zaɓe.

A cewarsa, matsalolin da ke cikin tsarin zaɓe da wasu hukumomin ƙasar na nuna cewa akwai buƙatar yin gyare-gyare cikin gaggawa domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da gaskiya, adalci da sahihancin zaɓe a Najeriya.

Advertisement

 

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending