News
Hisbah Za Ta Fara Wani Gagarumin Samame Mai Suna “Operation Kano First “
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da fara wani sabon gagarumin shiri na yaƙi da ayyukan lalata da sauran abubuwan da suka saɓa wa dokoki da al’adun jihar, wanda ta sanya wa suna “Operation Kano First.”
Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahid Aminuddeen, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa hukumar gudunmawar motoci 10 da babura 50 domin ƙarfafa ayyukanta.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 10 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Jigawa
Aminuddeen ya ce Hukumar Hisbah za ta ƙara tsaurara sa ido tare da ɗaukar matakan da suka dace kan duk wanda aka samu yana aikata abubuwan da ta bayyana a matsayin rashin ɗa’a.
Ya gargadi masu aikata irin waɗannan abubuwa da su sauya halayensu, yana mai cewa an fara aiwatar da “Operation Kano First”, kuma duk wanda aka kama zai fuskanci matakin doka.
Ya bayyana cewa jami’an Hisbah sun fara sintiri a manyan titunan birnin Kano a ranar Alhamis, a matsayin wani ɓangare na fara aiwatar da sabon shirin.
A cewarsa, sintirin zai ci gaba a kwanaki masu zuwa, domin ƙara wayar da kan jama’a kan bin doka, guje wa munanan ɗabi’u da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Mataimakin Kwamandan ɗin ya ƙara da cewa shirin zai kuma mayar da hankali wajen sasanta rikice-rikice tsakanin jama’a da kuma ƙarfafa zaman lafiya.
Hukumar Hisbah, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa, na da alhakin sa ido kan aiwatar da dokokin da suka shafi Shari’a, inganta kyawawan ɗabi’u da kuma taimakawa wajen sasanta rikice-rikicen al’umma.
Ana sa ran motocin da baburan da gwamnatin jihar ta bai wa hukumar za su ƙara mata ƙarfin gudanar da sintiri, sa ido a wuraren taruwar jama’a da kuma gaggauta kai ɗauki ga korafe-korafen jama’a.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
