Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Aike Da Kudirin Dokar Kafa ‘Yansandan Jihohi Ga Majalisar Dattawa 

Published

on

Tinubu Tinubu sign 750x430

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa kudirin dokar gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da ke neman kafa rundunar ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar.

Kudirin na neman yin gyara ga wasu sassa na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 domin samar da damar doka ga jihohi su kafa rundunonin ’yan sanda da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a yankunansu.

Advertisement

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci.

A lokuta da dama, Shugaba Tinubu ya nuna goyon bayansa ga kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa tsarin zai ba gwamnatocin jihohi damar taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin tsaro da suka shafi yankunansu.

Advertisement

A jawabinsa na ranar Dimokuraɗiyya da aka gudanar a wannan watan, Tinubu ya ce gwamnatinsa na ci gaba da ɗaukar matakan murƙushe masu aikata laifuka, inda ya bayyana cewa sama da ’yan ta’adda 13,000 aka kashe a cikin shekara guda da ta gabata.

Sai dai shugaban ƙasar ya amince cewa har yanzu akwai ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar, musamman batun mutanen da aka yi garkuwa da su, ciki har da wasu ɗalibai da ke hannun masu garkuwa a jihohin Oyo da Borno.

Advertisement

Batun kafa ’yan sandan jihohi ya daɗe yana jawo muhawara a Najeriya, inda masu goyon baya ke ganin zai taimaka wajen kusantar jami’an tsaro da al’umma, yayin da wasu ke nuna fargabar yiwuwar amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa.

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta fara nazarin kudirin nan ba da jimawa ba, lamarin da ka iya zama wani muhimmin mataki a tarihin gyaran tsarin tsaro a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending