Connect with us

News

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 A Kebbi

Published

on

images (2)

Aƙalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a garin Gulma da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan wasu shanu sun shiga gonar shinkafa ta wani manomi mai suna Alhaji Aminu, mai kimanin shekara 35, inda aka ce ya ji wa wata saniya rauni a yayin ƙoƙarin korar dabbobin daga gonarsa.

Advertisement

Yadda Wata Budurwa Ta Hallaka Kanta Bayan Rabuwa Da Saurayin Da Ta Dade Tana Soyayya Da Shi

Wata majiya daga garin ta shaida wa Jaridar Blueprint cewa tun bayan faruwar lamarin ne aka samu rashin jituwa tsakanin manomin da mai shanun. A ranar Litinin bayan Sallar Azahar, an ce su biyun sun sake haɗuwa a gonar, inda takaddama ta rikide zuwa faɗa.

Advertisement

Majiyar ta ƙara da cewa bayan manomin ya fi ƙarfin makiyayin a fafatawar, makiyayin ya zaro wuƙa tare da caka masa ita a ciki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.

Bayan samun labarin kisan, wasu fusatattun matasa daga garin sun fito da makamai tare da kai farmaki kan makiyayan da ke yankin. Rahotanni sun tabbatar da cewa makiyaya huɗu sun mutu a harin ramuwar gayya, yayin da aka kuma ƙona gawar wanda ake zargin ya kashe manomin.

Advertisement

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, ASP Nafiu Abubakar, ya ce tuni jami’an tsaro suka isa yankin domin shawo kan rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce an kama wasu mutane daga bangarorin biyu domin taimaka wa binciken da ake gudanarwa, yayin da aka tura jami’an soja da na ’yan sanda zuwa garin domin hana rikicin ƙara ta’azzara.

Advertisement

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aika masa ba domin jin ta bakinsa kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending