News
Rikicin Manoma da Makiyaya: Gwamna Buni Ya Ƙaddamar da Rugar Fulani a Nguru
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da wani sabon matsuguni na Rugar Fulani a Karamar Hukumar Nguru, a wani mataki da gwamnati ke fatan zai taimaka wajen rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Matsugunin, wanda shahararren mai taimakon al’umma Alhaji Balarabe Abdullahi (Balarabe DJ) ya assasa, an ce an tsara shi ne domin samar da mafita mai ɗorewa ga tashe-tashen hankula da ke da nasaba da kiwo a fili da lalata gonaki.
Rashin Shigar Mutane Masu Nagarta Siyasa Na Barin Mulki Hannun Marasa Kishin Kasa — Dr Getso
A cewar bayanan da aka gabatar yayin ƙaddamar da shirin, Rugar Fulani ɗin na ɗauke da muhimman kayayyakin more rayuwa da suka haɗa da gidaje masu ɗaki biyu, makaranta, cibiyar kasuwanci, cibiyar kula da lafiya ta matakin farko, ruwan sha, wutar lantarki da masallaci, domin sauƙaƙa rayuwar makiyaya da inganta zamantakewarsu.
Da yake jawabi, Gwamna Buni ya ce shirin zai taimaka wajen takaita kiwo a fili, wanda a lokuta da dama ke haddasa lalacewar gonaki da kuma rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma.
Ya ƙara da cewa samar da kiwo na zamani a yankunan karkara zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen shigar da makiyaya cikin tsarin rayuwar al’umma, tare da inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya a tsakanin su.
Gwamnan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa, musamman masu hannu da shuni, da su rungumi irin wannan yunƙuri da ke tallafa wa zaman lafiya da ci gaban al’umma.
“Mun lura da tasirin shirin da kuma amfanin da yake kawowa al’umma. Samar da makarantu, cibiyoyin lafiya, asibiti da gidaje a cikin Rugar, abin a yaba ne matuƙa,” in ji Gwamna Buni.
“Muna miƙa godiya a madadin al’ummar Karamar Hukumar Nguru, Jihar Yobe da ma Najeriya baki ɗaya.”
Tun da farko, Alhaji Balarabe Abdullahi ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin rage rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma, ta hanyar samar da wuraren kiwo na dindindin da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna.
