News
Sare Bishiyoyi A ARTV Ya Bankado Matsalolin Da Ke Addabar Tashar — Gwamnatin Kano
Wani labarin da ya karade kafafen sada zumunta kan sare bishiyoyi a harabar Abubakar Rimi Television (ARTV) ya jawo hankalin Gwamnatin Jihar Kano, inda lamarin ya kuma bankado wasu matsaloli da ke addabar tashar talabijin mallakin jihar.
A yayin wata ziyara ba-zata da ya kai tashar, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayar da umarnin dakatar da sare bishiyoyin nan take, yana mai bayyana aikin a matsayin wanda ya ci karo da manufofin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na kare muhalli da yaki da sauyin yanayi.
Kazafin Satar Mace Ya Janyo Wa Dan Acaba Duka
Ya umarci cewa daga yanzu babu wata bishiya da za a sare a harabar tashar ba tare da samun amincewar hukumomin gwamnati da abin ya shafa ba, yana mai gargadin cewa lalata muhalli na iya haifar da mummunan tasiri ga rayuwar al’umma.
Sai dai baya ga batun sare bishiyoyin, ziyarar ta kuma gano matsaloli masu yawa da suka dabaibaye ARTV, wadda a baya ta kasance daya daga cikin fitattun tashoshin yada labarai a Arewacin Najeriya.
Kwamared Waiya ya bayyana cewa bayanan da ma’aikatar sa ta tattara sun nuna cewa tashar na kasa biyan bukatun masu kallo saboda tsofaffin shirye-shirye, raunin ingancin samar da labarai da kuma rashin saurin rungumar fasahar zamani.
A cewarsa, yayin da yawancin tashoshin talabijin ke amfani da sabbin hanyoyin sadarwa da fasahar dijital domin karfafa hulda da masu kallo da kuma samar da damar kallon shirye-shirye a kowane lokaci, har yanzu ARTV na tafiyar da ayyukanta da tsarin da ya dade yana hana ta gogayya da sauran kafafen yada labarai na zamani.
“Wannan yanayi bai dace da hangen nesan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba, wadda ta mayar da hankali kan kirkire-kirkire, dijitalizashan da inganta ayyukan gwamnati a kowane fanni,” in ji shi.
Kwamishinan ya kuma bukaci mahukuntan tashar da su yi amfani da kudaden da ake ware musu wajen horas da ma’aikata, sabunta kayan aiki da aiwatar da gyare-gyaren da za su taimaka wajen dawo da martabar tashar.
A cewarsa, zai gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf rahoto na musamman domin neman goyon bayan gwamnati wajen aiwatar da cikakken shirin sauya tsarin ARTV zuwa na zamani domin inganta ayyukanta da kara ingancin hidimar da take bayarwa.
Haka kuma ya jaddada bukatar tabbatar da gaskiya, rikon amana da ingantaccen tsarin tafiyar da ma’aikata domin bunkasa aikin tashar.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Mataimakin Manajan Daraktan ARTV, Malam Idris Abba Musa, ya amince cewa tashar na fuskantar kalubale da dama da suka hada da tsaikon gudanarwa, karancin horaswa ga ma’aikata da kuma rashin wadataccen tsarin dijital.
Sanarwar ziyarar, wadda Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ameen Kabeer Yassar, ya sanya wa hannu, ta nuna cewa gwamnatin jihar na duba hanyoyin da za su taimaka wajen farfado da tashar.
Masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai na ganin cewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka zai sake bude tattaunawa kan makomar kafafen yada labarai mallakin gwamnati da kuma muhimmancin sabunta su domin dacewa da sauye-sauyen zamani.
