Connect with us

News

ZAMFARA: Ƴanbindiga Sun Yi Garkuwa Da Dattijai 50 Da Suke Je Sulhu 

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Yanbindiga sun yi garkuwa da dattijan garin Magamin Diddi da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a jihar Zamfara su aƙalla 50 lokacin da suka je tattaunawar sulhu.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a ƙasar ta bayyana cewa bisa ga dukan alamu madugun ƴanbindiga mai suna Jammo ne ya yi garkuwa da mutanen a wani gadun daji da ake kira Muntsira. To sai dai shugaban ƙaramar hukumar ta Maradun Alhaji Bello Dosara, ya ce mutanen sun je wannan tattaunawar ce ba tare da sanin gwamnati ba.

Advertisement

Sare Bishiyoyi A ARTV Ya Bankado Matsalolin Da Ke Addabar Tashar — Gwamnatin Kano

Dosara ya ce tuni aka sako 11 daga cikin mutanen, yayin da sauran 39 ke ci gaba da kasancewa a hannunsu ƴanbindigar.

Advertisement

Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Maradun ya tabbatar da cewa, garin na Magamin Diddi ‘’ya jima ƙarƙashin mamayar da killacewar ƴanbindiga, illa kawai jama’a na da damar fita domin cin kasuwa sau ɗaya ne kawia a kowanne mako’’.

Ta la’akarin da tsamin alaƙa tsakanin ɓangarorin biyu, ‘’a gaskiya na yi mamakin jin cewa (waɗannan dattijai) sun yi tattaki domin ganawa da ƴanbindigar”.

Advertisement

A kwanakin da suka gabata ne aka ruwaito cewa an yi arangama tsakanin jami’an rundunar tabbatar da tsaro a jihar ta Zamfara da ake kira ‘’Askarawa” da kuma baraden Jammo, inda aka kashe ƴanbindigar da dama tare da ƙwace makamai daga gare su.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending