Connect with us

News

Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi

Published

on

mallam nasir el rufai governor of kaduna state nigeria

Likitan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Dakta Bello Abubakar, na fuskantar bincike daga hukumomin da ke kula da harkokin likitanci a Najeriya, bayan zargin bayar da rahoton jinya na bogi.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya biyo bayan gurfanar da likitan a gaban kotu da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta yi, bisa zargin gabatar da rahoton jinya da ake cewa ba sahihi ba domin tallafa wa buƙatar belin tsohon gwamnan a wata shari’a.

Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Biyu A Kan Babur 

A cewar ICPC, ana tuhumar Dakta Bello Abubakar da laifuka huɗu, ciki har da zargin bai wa jami’an gwamnati bayanan ƙarya da kuma amfani da rahoton jinya da ake zargin bai samu sahalewar Asibitin Ƙasa da ke Abuja ba.

Majiyoyi sun shaida cewa kafin gurfanar da likitan, ICPC ta nemi ƙwararrun likitoci daga Najeriya da Amurka su yi nazari kan rahoton, inda aka ce sun bayyana cewa rahoton bai cika ƙa’idodin ƙwararrun likitanci ba.

Haka kuma, takardun da aka gabatar a kotu sun nuna cewa ana sa ran Babban Daraktan Kula da Lafiya na Asibitin Ƙasa zai bayar da shaida cewa rahoton da ake magana a kai bai samu amincewar asibitin ba, kuma ba a bi hanyoyin da doka ta tanada wajen fitar da shi ba.

Advertisement

Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kotu ba ta yanke hukunci kan zarge-zargen ba, kuma ana ci gaba da sauraron shari’ar.

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending