Connect with us

News

Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Biyu A Kan Babur 

Published

on

crash 1024x770

Mutane biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Litinin a yankin Olorunsogo da ke unguwar Leme, a Karamar Hukumar Abeokuta ta Kudu, Jihar Ogun.

Rahotanni sun ce hatsarin ya afku da misalin karfe 5:45 na yamma, inda wata mota kirar Lexus ta yi karo da wani babur kirar TVS.

Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Biyu A Kan Bubar 

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa motar Lexus na tafiya cikin tsananin gudu lokacin da ta bugi babur din. Direban babur ya mutu nan take bayan ya samu mummunan rauni a kansa.

Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Ogun, Afolabi Odunsi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutane shida ne hatsarin  ya ritsa da su, amma mutum biyu ne suka rasu, yayin da sauran suka tsira ba tare da samun raunuka ba.

Ya kara da cewa an kai gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiye gawa na Asibitin Jiha da ke Ijaye, yayin da jami’an suka kwaso kayayyakin da aka samu a wurin, ciki har da katin shaida da wayar salula.

Advertisement

 

DAILY POST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending