Connect with us

News

Gwamnatin Tarrayya Ta Kashe Naira Biliyan 57.78 A Harkar Tsaro Cikin Watanni Hudu

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Gwamnatin Tarayya ta kashe kimanin naira biliyan 57.78 wajen ayyukan tsaro a cikin watanni huɗun farko na shekarar 2026, duk da cewa hare-haren ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane na ci gaba da addabar sassa daban-daban na ƙasar.

Bayanan hukuma da ke cikin dandalin Open Treasury Portal sun nuna cewa an kashe wannan kuɗi ne tsakanin watan Janairu da Afrilu, adadin da ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da naira biliyan 25.35 da aka kashe a daidai wannan lokaci a shekarar 2025.

Advertisement

Mutane 11 Sun Kamu Da Cutar Ƙwalara A Filato, Biyar Sun Rasu

Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen sun haɗa da sayen kayan aikin soji, inganta cibiyoyin tsaro, gina da gyaran barikin jami’an tsaro da kuma sauran ayyukan da suka shafi kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Advertisement

Sai dai duk da wannan ƙarin kashe kuɗi, matsalar tsaro na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale ga ƙasar. Rahotanni sun nuna cewa hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka na ci gaba da jefa al’umma cikin fargaba a yankuna da dama.

Wani rahoton tsaro na baya-bayan nan ya nuna cewa cikin mako guda kacal, an samu aukuwar laifuka 98 da suka haɗa da kisan kai, hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Advertisement

Jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Kebbi na daga cikin yankunan da suka fi fuskantar matsalar tsaro a halin yanzu. A wani lamari na baya-bayan nan, an ruwaito cewa wasu mutum 39 sun shiga hannun ‘yan bindiga a Jihar Zamfara bayan wani yunƙurin sasanta rikici da wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

NIGERIAN NEWS24

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending