Connect with us

News

Birtaniya, Faransa, Jamus da Italiya Na Shirin Janye Takunkumi Kan Iran

Published

on

FB IMG 1781529686511

Ƙasashen Biritaniya, France, Germany da Italy sun bayyana cewa a shirye suke su janye takunkuman da aka ƙaƙaba wa Iran.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar haɗin gwuiwa da suka fitar, inda suka yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya.

Advertisement

Mutane 11 Sun Kamu Da Cutar Ƙwalara A Filato, Biyar Sun Rasu

Sai dai ƙasashen sun jaddada cewa janye takunkumin zai dogara ne kan matakan da Iran za ta ɗauka, musamman kan shirinta na makamashin nukiliya, tare da tabbatar da cewa Tehran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.

Advertisement

Ana kallon wannan mataki a matsayin babbar nasara ta diflomasiyya wadda ka iya rage tashin hankali da kuma taimakawa wajen dawo da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending