News
Kotu Ta Umarci INEC Ta Soke Rajistar ADC Da Wasu Jam’iyyu 4
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyun siyasa guda biyar, ciki har da ADC, Accord, AA, APP da ZLP.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan ƙungiyar tsofaffin ‘yan majalisu ta kai ƙara tana neman kotu ta tilasta wa INEC aiwatar da tanadin doka kan jam’iyyun da suka gaza cika ƙa’idojin da kundin tsarin mulki ya gindaya.
Birtaniya, Faransa, Jamus da Italiya Na Shirin Janye Takunkumi Kan Iran
A cewar masu ƙarar, jam’iyyun sun gaza samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a zaɓe ko kuma samun kujeru a matakan gwamnati kamar yadda doka ta tanada, lamarin da ya sa kotun ta bayar da umarnin a cire su daga jerin jam’iyyun da aka amince da su.
Hukuncin na iya yin tasiri ga shirye-shiryen zaɓen 2027, musamman ga ‘yan takarar da ke shirin tsayawa takara a ƙarƙashin waɗannan jam’iyyu.
