News
Kotu Ta Daure Matar Tsohon Shugaban Kasar Koriya Ta Kudu A Gidan Yari Bayan Samunta Da Laifin Karbar Cin Hanci
Wata kotu a Koriya ta Kudu, ta yanke wa matar tsohon shugaban kasar Kim Keon Hee hukuncin daurin shekara daya da watanni takwas a gidan yari bayan samun ta da laifin karbar cin hanci daga Cocin Unification.
Kotun Gundumar Tsakiya ta Seoul ta ce Kim ta karɓi kuɗi da kyaututtuka masu tsada daga cocin da wasu masu hannu da shuni, da darajarsu ta kai aƙalla dala 200,000.
Amma kotun ta wanke ta daga wasu zarge-zarge da suka haɗa da sauya farashin hannun jari da kuma karya dokar kuɗaɗen siyasa.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa Cocin Unification ta bai wa Kim kyaututtuka masu daraja, ciki har da jakunkuna biyu na Chanel da abun wuya na lu’u-lu’u, a wani yunƙuri na samun tasiri a wajen matar shugaban ƙasa.
A kan wannan zargi ne aka gurfanar da shugabar cocin, Han Hak-ja, wadda ke fuskantar shari’a a halin yanzu.
A cewar masu gabatar da ƙara, Kim ta haɗa baki da ƙungiyar addini ta hanyar da ta saɓa wa ka’idar raba addini da gwamnati da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
Sai dai Kim ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba su da tushe.
Duk da haka, ta nemi afuwa a bainar jama’a, inda ta ce ta yi kura-kurai da dama duk da rawar da take takawa a wancan lokaci.
Mijinta, tsohon shugaban ƙasa Yoon Suk Yeol, an tsige shi daga mulki a shekarar da ta gabata, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar saboda rawar da ya taka wajen ayyana dokar ta-baci a watan Disambar 2024.
Har yanzu yana fuskantar wata shari’a dabam da ka iya kai shi ga hukuncin kisa.
A baya dai, a shekarar 2023, an fitar da wani bidiyo da aka ɗauka a ɓoye da ke nuna Kim na karɓar jakar Dior mai tsada, abin da ya jawo cece-kuce a ƙasar tare da raunana farin jinin gwamnatin mijinta.
