News
Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Shugaban Koriya Ta Kudu Hukuncin Daurin Shekaru 30
Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol, hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samunsa da laifin shirya tura jirage marasa matuƙa zuwa Koriya ta Arewa domin haddasa rikicin da zai ba shi damar aiwatar da manufofin siyasa.
Alƙalan kotun sun bayyana cewa Yoon ya amince da tura jiragen marasa matuƙan ne a shekarar 2024 domin tunzura North Korea ta ɗauki matakin soji kan South Korea. A cewar kotun, manufar hakan ita ce ƙara taɓarɓarewar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu da kuma haifar da tashin hankali a cikin gida.
DSS Ta Cafke Matashi Da Ke Safarar Bindigogin AK-47 Da Bom-Bom Na RPG A Kano
Kotun ta ƙara da cewa tsohon shugaban ya yi ƙoƙarin amfani da yanayin rikicin wajen tabbatar da ayyana dokar soja, matakin da ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin mulkinsa.
Sai dai Yoon ya musanta zarge-zargen da ake masa, yana mai cewa matakan da ya ɗauka sun kasance ne domin kare tsaron ƙasarsa. Haka kuma, lauyoyinsa sun ce tura jiragen marasa matuƙan martani ne ga abin da suka kira tsokana daga Koriya ta Arewa, bayan da ta aika balan-balan ɗauke da tarkace zuwa yankin Koriya ta Kudu.
Hukuncin da kotun ta yanke na daga cikin manyan shari’o’in siyasa da suka girgiza Koriya ta Kudu a ‘yan shekarun nan, tare da jawo muhawara kan yadda shugabanni ke amfani da ikon gwamnati a lokutan rikici.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News5 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
