Connect with us

News

Shetima zai yi balaguro zuwa kasar Afrika ta kudu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima zai yi balaguro zuwa birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu, domin wakiltar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a taron Shugabannin kungiyar kasashen BRICS karo na 15.

Advertisement

Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin a Abuja.

Peter Obi Ya Musanta Cewar Yana Tattaunawa Da Kwankwaso Da Atiku Domin Kafa Sabuwar Jam’iyya

Mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran shugabannin kasashe da ‘yan kasuwa da kuma ‘yan siyasa daga sassa daban daban na duniya a yayin taron da za’a yi a cibiyar taro ta Sandton dake birnin Johannesburg daga yau 22 ga wata zuwa 24 ga watan da muke ciki.

Advertisement

Taron kasashen kungiyar BRICS, ya kunshi kasashen Brazil da Rasha da India sai China da Afrika ta kudu wanda suka cure wuri daya a kokarin da inganta tattalin arzikin duniya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending