Connect with us

News

Koriya Ta Arewa Za Ta Taimaka Wa Iran Wajen Gyara Tashoshin Nukiliyarta

Published

on

d286fe6cce43f30113cde06fe2499a35277262f0de5b0d5e0ee53c06eccfe7ce

Wani masani kan harkokin tsaro ya bayyana cewa akwai yiwuwar ƙasar Koriya ta Arewa za ta taimaka wa Iran wajen gyara tashoshin nukiliyarta da hare-haren Amurka suka lalata, tare da gina sababbin masana’antun makamai masu linzami a ƙasar.

Masanin, Ankit Panda, daga Cibiyar Tsaro ta Kasa da Kasa da ke Amurka, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wannan mataki na Koriya ta Arewa zai iya rage matsin lamba da kasashen Yamma ke dora wa Iran dangane da shirinta na nukiliya.

Advertisement

Ba A Fadawa Tinubu Gaskiyar Halin Da Ƴan Najeriya Ke Ciki — Usman Bugaje

Koriya ta Arewa ta caccaki Amurka

A baya-bayan nan, Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta fito da wata sanarwa tana sukar harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliya a Iran, tana mai cewa hakan keta hurumin ‘yancin kai ne da kuma tsaron ƙasar Iran.

Advertisement

Sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa, KCNA, ya fitar ta ce:

“Amurka da Isra’ila su ne ginshikin rikicin Gabas ta Tsakiya, musamman ta hanyar yunkurin faɗaɗa ikon Isra’ila da samun goyon bayan kasashen Yamma.”

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa kamata ya yi al’ummomin duniya masu kishin adalci su fito su ƙalubalanci irin waɗannan ayyuka tare da ɗaukar mataki.

Dangantakar soji tsakanin Iran da Koriya ta Arewa

Advertisement

Koriya ta Arewa da Iran sun daɗe suna hulɗa ta fuskar soji, kuma rahotanni sun ce akwai musayar fasahar kera makamai masu linzami tsakanin su.

Sai dai Ankit Panda ya ce ba lallai Koriya ta Arewa ta taimaka wa Iran kai tsaye wajen haɓaka makaman nukiliyarta ba, domin hakan na iya sanya fasahar ta fadawa hannun Amurka, wanda zai iya bayyana sirrin fasahar makaman Koriya ta Arewa.

Advertisement

Duk da haka, masanin ya nuna yiwuwar Koriya ta Arewar za ta iya taka rawa a fannin gyare-gyare da horarwa, la’akari da ƙwarewarta a fasahar makamai da kuma kasancewarta abokiyar hulɗa ta dogon lokaci da Iran da Rasha.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending