Sports
Ruftawar Gini A Kano: Ana Fargabar Mutane Takwas Sun Mutu A Ghari
Ana fargabar cewa mutane akalla takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon ruftawar wani gini a garin Ridawa da ke ƙaramar hukumar Ghari a jihar Kano.
Rahotanni daga majiyar Premier Radio sun ce lamarin ya faru ne a wani lokaci da ba a tantance ba, inda ginin ya rufta dauke da mutane a ciki.
An haifi jarirai sama da 36,000 a Kano cikin watanni 9 — Gwamnatin Tarayya
A cewar majiyoyin yankin, ana ci gaba da aikin ceto domin gano wadanda suka makale a karkashin baraguzan ginin, yayin da aka fara tono wasu gawarwaki.
Har zuwa yanzu, ba a fitar da cikakken bayani daga hukumomi kan musabbabin ruftawar ginin ba, sai dai ana sa ran za a gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa lamarin.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
