News
An haifi jarirai sama da 36,000 a Kano cikin watanni 9 — Gwamnatin Tarayya
Hukumar kidaya ta Nijeriya (NPC) ta ce ta yi rijistar haihuwar yara sama da 36,000 a Kano cikin watanni tara da fara amfani da tsarin rijistar haihuwa ta na’ura.
Daraktan hukumar a jihar, Balarabe Kabir ne ya bayyana hakan a wani taron horas da masu horaswa da aka gudanar a Kano.
Ya ce an shirya taron ne da hadin gwiwar kungiyar kananan hukumomi ta Nijeriya da hukumar da ke rijistar katin dan kasa (NIMC), tare da tallafin gwamnatin Netherlands da kuma UNICEF.
DSS Sun Kubutar Da Sakataren Karamar Hukumar Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Kano
Kabir ya bayyana cewa adadin da aka bayar wani bangare ne kawai na yawan yaran da aka riga aka yi wa rijista, inda ya kara da cewa an kuma tantance yara kusan 27,000 ‘yan kasa da shekaru biyar, da sama da 40,000 da suka haura wannan shekaru, wadanda ba a taba rijistar su ba a baya.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
