News
Dakarun Soji Sun Kama Uba Da Ɗansa Kan Zargin Alaƙa Da ’Yan Ta’adda A Sakkwato

Dakarun sojin Najeriya sun cafke wani mutum da ɗansa bisa zargin alaƙa da ƙungiyoyin ’yan ta’adda a Jihar Sakkwato.
An kama waɗanda ake zargin, Muhammadu Ali da ɗansa Umaru Ali, da misalin ƙarfe 12:47 na daren ranar 11 ga Nuwamba, 2026, a dajin Bauni da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza ta jihar.
Rikici Ya Tilasta Mutane Sama Da Dubu 6,000 Ƙetara Wa Nijar Daga Najeriya A Cikin Shekara Guda
Zagazola Makama ya rawaito cewa dakarun Bataliya ta 248 ne suka gudanar da samamen tare da haɗin gwiwar tawagar yaƙi da ta’addanci ta National Counter Terrorism Centre.
A yayin samamen, jami’an tsaron sun ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya,mai ɗauke da harsasai uku na musamman kirar 7.62mm, da kuma kuɗi naira 9,760.
Rahoton ya ce ana zargin mutanen biyu da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, sai dai har yanzu ba a fayyace irin rawar da suke takawa ko girman alaƙar tasu ba.
